Shari’ar El-Zakzaky:An Haramta Gangami A Kaduna

 0 44
Rundunar ‘yan sandan Kaduna ta haramta yin gangami a yayin da za a ci gaba d shari’ar Shugaban Kungiyar ‘Yan Shi’a, Malam Ibrahim El Zakzaky a yau Laraba.
Kakakin Rundunar, DSP Mukhtar Aliyu ya ce za a girke jami’an ‘yan sanda a muhimman wurare a cikin birnin don ganin ba a samu hatsaniya ba inda ya nemi al’ummar jihar kan su sanya ido a kan duk wanda ba su amince da shi ba.

#Rariya

0 Comments

Newest